Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki matakan inganta hukumomin tsaron Najeriya domin tabbatar da an magance tabarbarewar tsaro yadda ya kamata.
Ya bayyana hakan ne a taron ƙara wa juna sani na manyan jami’an ‘yan sanda na ƙasa karo na biyar, wanda aka gudanar a Abeokuta, Jihar Ogun.
Tinubu, wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya ce gwamnatin sa ta fahimci muhimmancin tsaro wajen farfaɗo da tattalin arziƙi, wanda ya sa aka samar da kayan aiki na zamani ga jami’an tsaro don su iya ɗaukar matakan gaggawa idan an samu barazana.
Shugaban kasar ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya su haɗa kai da gwamnati ta hanyar ba da goyon baya ga jami’an tsaro don cimma burin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.
