Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Malam Ibrahim Khalil, ya tabbatar da cewa Sheikh Muhammad Bin Usman zai ci gaba da jagorantar salloli a tsohon Masallacin Sahaba da ke Kundila.
A cewarsa, bayan tattaunawa da bangarorin da ke takaddama kan Masallacin Jami’ur Rahman, an yanke shawarar cewa Ay Mai Kifi da mukarrabansa za su ci gaba da kula da al’amuran masallacin Jami’ur Rahman, yayin da Sheikh Muhammad Bin Usman zai koma tsohon masallacinsa.
Malam Ibrahim Khalil ya gode wa jami’an tsaro bisa rawar da suka taka wajen hana tashin hankali yayin rikicin da ya taso a masallacin.
