Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce jam’iyyar APC tana samun karɓuwa a Najeriya sakamakon gudanar da mulkin adalci tun daga matakin jiha har zuwa tarayya.
Ya bayyana haka ne a jiya Asabar yayin karɓar wasu manyan ’yan siyasa 50 da suka sauya sheka daga wasu jam’iyyu zuwa APC a Kaduna. Gwamnan ya tabbatar musu da cewa za a yi tafiya dasu ba tare da bambanci ba.
Cikin wadanda suka koma APC har da tsohon gwamnan Kaduna, Muktar Ramalan Yero, Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi, dan takarar gwamna na NNPP a zaben da ya gabata, Alhaji Sani Sha’aban, Sanata Danjuma Laah, da Abubakar Mustapha, tsohon sakataren PDP na ƙasa.
Taron sauya shekar ya gudana a dandalin Murtala Square, Kaduna, a ranar Asabar.
