Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, murnar cika shekaru 65 da haihuwa, yana mai jinjina masa kan gudunmawar da ya bayar ga cigaban dimokuraɗiyya a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a fannin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Lahadi, Tinubu ya bayyana El-Rufai a matsayin malami kuma hazikin dan siyasa. Ya kuma yaba da rawar da ya taka wajen kafa jam’iyyar APC da nasarorin da jam’iyyar ta samu a zabukan 2015, 2019, da 2023.
