Masu garkuwa da mutanen da suka sace daraktan mulki na jam’iyyar APC a matakin ƙasa, Dr. Raif Adeniji, sun nemi a biya su kuɗin fansa naira miliyan 350 kafin su sake shi.
Sun tuntuɓi iyalansa, suna mai jaddada cewa ba za su sako shi ba sai an biya wannan kuɗi, kamar yadda wata majiya daga danginsa ta bayyana.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace Adeniji tare da ɗan uwansa, matar ɗan uwansa, da dansa, a Kubwa, Abuja. Sai dai daga bisani, an gano gawar matar ɗan uwansa a Tafa, Jihar Neja.
Har yanzu, rundunar ‘yan sanda ta Abuja ba ta yi jawabi kan lamarin ba.
