DSS Ta Gayyaci Sheikh Muhammad Bin Uthman Bayan Dakatar
Hukumar gudanarwar Masallacin Jami’ur Rahman, wanda a baya aka fi sani da Masallacin Sahaba, ta dakatar da Sheikh Muhammad Bin Usman daga limanci, bayan gabatar da hudubar da ta haifar da rudani a ranar 24 ga Janairu, 2025. Sheikh Usman, wanda ya jagoranci limancin Masallacin Sahaba na tsawon shekara 24, ya kasance a matsayin babban limami a sabon masallacin da AY Maikifi ya gina.
A yayin hudubar, Sheikh Usman ya bayyana yadda aka mayar da shi saniyar ware a cikin gudanarwar masallacin, inda ya koka cewa hukumomin masallacin sun naɗa limamai uku ba tare da sanya shi a matsayin shugaba ba. Wannan jawabi ya fusata wasu daga cikin masu yin Sallah, har da kokarin farmakar sakataren kwamitin masallacin, Abdulkadir Isawa.
A sakamakon haka, hukumar masallacin ta aikewa da Sheikh Usman wasikar dakatar da shi daga limanci. Wasikar ta ce dakatarwar ta biyo bayan rudanin da hudubarsa ta haifar.
A ranar Litinin, DSS da mahukuntan masallacin sun gayyaci Sheikh Usman, inda aka ja kunnen sa game da hudubobin da za su iya haifar da tashin hankali. Majalisar Malamai ta kuma shawarci Sheikh Usman da ya koma tsohon Masallacin Sahaba, amma har yanzu ba a samu tabbacin ko zai amince da wannan shawara ba.
source:Daily Nigerian
By:
