Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi amfani da taken wasu wakoki daga sabon kundin waƙoƙin ɗan uwansa Davido mai suna “Oriadé” wajen isar da saƙon yakin neman zaɓensa na wa’adi na biyu.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Adeleke ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar samun nasara a zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
Gwamnan ya ce kiran da yake yi na zaman lafiya ba alamar rauni ba ne, yana mai jaddada cewa ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar za su tabbatar da nasararsa.
Ya yi amfani da kalmomi da taken waƙoƙin da ke cikin kundin Oriadé, ciki har da “I Know Who I Be,” “Amazing Grace,” “On the Road,” “Tell Everybody,” “Already Falling,” “Yaya,” da “Gimme Dat Ting”, wajen bayyana yakin neman zaɓensa.
Adeleke ya kuma yi ikirarin cewa babu wanda zai kwace masa kujerar gwamna, yana mai cewa jama’ar Osun sun san irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi.
Sabon kundin Oriadé na Davido, wanda shi ne kundinsa na shida, ya ƙunshi waƙoƙi 13 kuma an fitar da shi ne domin cika shekaru 15 da fara harkar kiɗansa.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar zazzafar siyasa da kuma shirye-shiryen zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2026.
