Kamfanin sadarwa na Airtel Nigeria ya sanar da faɗaɗa cibiyoyin sayar da kayayyaki da rarraba ayyukansa a faɗin ƙasar domin inganta hidima ga kwastomomi da kuma biyan buƙatar da ke ƙaruwa na ayyukan sadarwa da na zamani.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa cibiyoyin sayar da kayayyakinsa yanzu sun kai fiye da shagunan Airtel 4,000, tare da sama da cibiyoyin hidima 200,000 a faɗin Najeriya, ciki har da shagunan haɗin gwiwa, wakilan kasuwanci da dillalan unguwanni.
Sabuwar faɗaɗawar za ta bai wa masu amfani damar samun ayyuka kamar rajistar layin SIM, sayen wayoyi, sayen katin waya da data, samun tallafin kwastomomi da sauran ayyukan dijital cikin sauƙi a wuraren da suke zaune ko aiki.
Babban Jami’in Kamfanin Airtel Nigeria, Dinesh Balsingh, ya ce samar da ingantaccen sabis na sadarwa ba ya tsaya ga gina hasumiyoyin sadarwa kawai, illa kuma yana buƙatar kusantar kwastomomi.
Ya ce kamfanin zai ci gaba da saka hannun jari wajen ƙarfafa cibiyoyin rarraba kayayyaki domin tabbatar da cewa kowane kwastoma yana samun ingantacciyar hidima a duk inda yake.
A nasa bangaren, Daraktan Sashen Tallace-tallace da Rarrabawa na Airtel Nigeria, Joypratip Sengupta, ya bayyana cewa nasarar cibiyar rarraba kayayyakin kamfanin ta samo asali ne daga ingantaccen tsarin jigilar kaya, haɗin gwiwa da abokan hulɗa, da kuma kusanci da al’ummomi.
Ya ce wannan tsarin na taimaka wa Airtel wajen isar da ayyukansa cikin sauri da inganci tare da biyan bukatun kwastomomi a sassa daban-daban na Najeriya.
