Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu haɗuwar rana, gajimare da kuma ruwan sama mai tsawa a sassa daban-daban na ƙasar daga ranar Lahadi zuwa Talata.
A hasashen yanayin da hukumar ta fitar a Abuja, ta ce a ranar Lahadi za a samu hasken rana tare da gajimare a yawancin jihohin Arewa, yayin da ake sa ran za a yi ruwan sama mai tsaka-tsaki tare da tsawa a wasu sassan jihohin Taraba, Adamawa da Kaduna da safe.
Da yamma kuma, ana sa ran ruwan sama mai tsawa zai sauka a wasu sassan Borno, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina, Kano, Kaduna, Adamawa da Taraba.
A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai tsawa a wasu sassan Plateau, Niger, Nasarawa da Babban Birnin Tarayya (FCT) da safe, yayin da da yamma za a samu irin wannan yanayi a Kogi, Benue, Plateau, Niger, Nasarawa da FCT.
A Kudancin ƙasar, ana sa ran za a yi ruwan sama a wasu sassan Ondo, Ogun, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, Lagos da Bayelsa da safe, kafin ruwan ya bazu zuwa kusan dukkan jihohin yankin da yamma.
A ranar Litinin, NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai tsawa a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Adamawa da Taraba da safe, sannan daga baya ya bazu zuwa Borno, Jigawa, Yobe, Bauchi, Gombe, Kano, Katsina, Kaduna, Taraba da Adamawa.
A ranar Talata kuma, ana sa ran za a samu gajimare a yankin Arewa tare da yiwuwar ruwan sama mai sauƙi a Bauchi, Jigawa da Yobe da safe, yayin da daga baya za a samu ruwan sama mai tsaka-tsaki a yankuna da dama.
NiMet ta kuma yi gargadin cewa ci gaba da samun ruwan sama a yankunan gabar teku na Kudancin Najeriya na iya haifar da ambaliyar ruwa cikin gaggawa, tare da shawartar jama’a da su guji tuki ko tafiya cikin ruwan ambaliya.
Hukumar ta kuma buƙaci mutane su ɗaure abubuwan da iska za ta iya kwashewa, su cire kayan lantarki daga wutar lantarki lokacin tsawa, sannan su guji tsayawa ƙarƙashin manyan bishiyoyi domin kauce wa haɗari.
Hakazalika, NiMet ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su riƙa samun rahoton yanayi na filayen jiragen sama daga hukumar domin sauƙaƙa tsare-tsaren tafiyar jirage.
