Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, kuma Shugaban Kamfanin Portland Gas Limited, Alhaji Lai Mohammed, ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta samar da tabbatattun dokoki, manufofi masu gaskiya da kuma tsarin haraji mai jan hankali domin jawo jarin da ake buƙata wajen bunƙasa fannin makamashin ƙasar.
Lai Mohammed ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a taron Oriental News Nigeria 2026 Conference da aka gudanar a Legas.
A jawabinsa mai taken “Carbon Capture: Accelerating Decarbonisation Initiatives in Nigeria’s Extractive Industry Through Broad Regulatory Reforms,” ya ce rage gurɓatar muhalli (decarbonisation) ya zama muhimmin abin da ya kamata a aiwatar cikin gaggawa, ba wai buri na nan gaba kawai ba.
Ya bayyana cewa amfani da fasahar Carbon Capture, makamashi mai tsafta da kuma gyaran dokoki na da matuƙar muhimmanci wajen cimma burin Najeriya na sauya zuwa tsarin makamashi mai ɗorewa.
A cewarsa, gina ababen more rayuwa kaɗai ba zai wadatar wajen cimma burin kare muhalli da rage hayaƙin carbon ba, yana mai jaddada cewa akwai buƙatar ingantaccen tsarin zuba jari, dorewar ayyuka da kuma kyakkyawan shugabanci kan batutuwan sauyin yanayi.
Lai Mohammed ya ce babban ƙalubalen da ke hana bunƙasa ayyukan makamashi mai tsafta a Afirka shi ne ƙarancin kuɗaɗen zuba jari.
Ya ce akwai buƙatar samar da sabbin hanyoyin samun kuɗi, ciki har da haɗa jarin gwamnati da masu zaman kansu, Green Bonds, kasuwannin carbon da kuma tsare-tsaren zuba jari na dogon lokaci domin rage haɗarin ayyuka da ƙara jan hankalin masu zuba jari.
Shi ma Manajan Darakta na Sahara Group, Injiniya Kola Adeshina, ya bayyana cewa taken taron ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar ɗaukar matakai na zahiri kan rage hayaƙin carbon.
Ya ce Najeriya na da damar aiwatar da ayyukan Carbon Capture, amma hakan zai yiwu ne idan an samar da ingantattun dokoki, bayanai masu inganci, tsarin tattalin arziki mai ƙarfi da kuma ka’idojin gudanar da ayyuka masu kyau.
Adeshina ya ƙara da cewa dole ne a koma daga tsara manufofi zuwa aiwatar da ayyuka, daga magana zuwa samar da jari, sannan daga buri zuwa sakamako mai auna.
A nata jawabin, Mai Wallafa Oriental News Nigeria Online, Yemisi Izuora, ta ce duk da muhimmancin masana’antar albarkatun ƙasa ga tattalin arzikin Najeriya, ya zama wajibi a tabbatar da cewa ana sarrafa albarkatun cikin hanyar da za ta kare muhalli da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
