Tsohon Shugaban Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Gombe, Hon. Danladi Ya’u, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tare da komawa Peoples Democratic Party (PDP), inda ya bayyana cikakken goyon bayansa ga takarar gwamna ta Farfesa Isa Ali Pantami a zaben shekarar 2027.
Danladi Ya’u, wanda a halin yanzu yake matsayin Mai Binciken Kudi (State Auditor) na ADC a jihar, ya bayyana matakin nasa ne cikin wata takardar murabus da ya aikawa shugaban jam’iyyar na mazabarsa a Kwadon, karamar hukumar Yamaltu/Deba.
A cikin takardar, ya ce murabus dinsa ya fara aiki nan take, wanda ya kawo karshen mukaminsa da kuma kasancewarsa mamba a jam’iyyar ADC.
Ya bayyana cewa ya koma PDP ne domin mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya, yana mai cewa tsohon Ministan Sadarwa ne ya fi dacewa da jagorantar Jihar Gombe bayan zaben 2027.
Danladi Ya’u ya kuma gode wa shugabanni da mambobin ADC bisa damar da suka ba shi na yin aiki tare da su, yana mai cewa abubuwan da ya koya da dangantakar da ya gina a jam’iyyar za su kasance abin tunawa a gare shi.
A karshe, ya yi wa jam’iyyar ADC da shugabanninta fatan alheri a kokarinsu na gaba.
