Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, da Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, sun yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su dauki matakan da za su tabbatar da adalci da ci gaba ga yankin Neja Delta, bayan shekaru 70 na hako man fetur a yankin.
Sun bayyana hakan ne a wajen taron Sweet Crude Dialogue 2026 da aka gudanar a Yenagoa, mai taken “Through the Python’s Eye: 70 Years of Oil and Gas Production in Nigeria.”
A jawabin da mataimakin gwamnan Bayelsa, Dr. Peter Akpe, ya gabatar a madadin Gwamna Diri, ya ce yankin Neja Delta ya fuskanci mummunar lalacewar muhalli sakamakon zubar danyen mai tsawon shekaru.
Ya bayyana cewa rahoton Hukumar Bayelsa State Oil and Environment Commission ya nuna cewa tsakanin shekarar 1958 zuwa 2010, an zubar da kusan gangunan danyen mai miliyan 13 a yankin, lamarin da ya haifar da babbar illa ga muhalli da rayuwar al’umma.
Gwamnan ya bukaci kungiyoyin kare muhalli da su hada hannu da gwamnati domin aiwatar da shawarwarin da rahoton ya bayar, tare da tabbatar da gyaran kasa, ruwa da kuma dawo da hanyoyin samun rayuwa ga al’ummomin yankin.
A nasa jawabin, Goodluck Jonathan ya ce Najeriya ba za ta samu cikakken ci gaba daga bangaren mai ba muddin ba ta fara kera kayan aikin masana’antar mai a cikin gida ba.
Ya ce dogaro da fitar da danyen mai kadai ba zai samar da wadatattun ayyukan yi ko bunkasa tattalin arziki ba, yana mai jaddada muhimmancin dokar Local Content Act da gwamnatinsa ta kafa da kuma Petroleum Industry Act (PIA).
Shi ma masani kan dokokin man fetur, Farfesa Ibibia Worika, ya ce duk da dimbin kudaden da Najeriya ta samu daga man fetur cikin shekaru 70, yankin Neja Delta bai samu ci gaban da ya dace ba.
Ya kara da cewa tabbatar da adalcin muhalli ga yankin ba kawai wajibi ne na doka ba, har ila yau wajibi ne na ci gaba da mutunta hakkin al’umma.
