Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya shawarci masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da su daina dogaro da neman aikin gwamnati ko kamfanoni bayan sun kammala hidimarsu, maimakon haka su rungumi harkokin kasuwanci da koyon sana’o’i domin su zama masu samar da ayyukan yi.
Ya bayyana cewa a halin yanzu sana’a da kasuwanci sun fi samar da damar samun kuɗi da dogaro da kai fiye da jiran aikin farin kwala, tare da ƙarfafa matasa su yi amfani da shirin Skills Acquisition and Entrepreneurship Development (SAED) na NYSC.
Gwamnan ya kuma yabawa masu yi wa ƙasa hidima da ke aiki a jihar saboda jajircewarsu, yayin da Darakta Janar na NYSC ya bukaci masu ɗaukar su aiki su tabbatar da jin daɗinsu ta hanyar samar da masauki, tsaro, lafiya da yanayin aiki mai kyau.
Masu ruwa da tsaki sun jaddada cewa koyon sana’a da kasuwanci na daga cikin hanyoyin magance matsalar rashin aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
