Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta tabbatar da kwato wata bindiga ba bisa ka’ida ba tare da harsasai takwas a gidan wani mutum mai suna Edet George da ke ƙauyen Ikot Akpan Afaha, karamar hukumar Uyo.
A cewar rundunar, jami’anta sun kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa mutumin yana amfani da bindigar wajen tsoratar da mazauna yankin. Bayan binciken gidan, an gano bindigar da alburusan a ɓoye.
Binciken farko ya kuma nuna cewa matar wanda ake zargin ta shaida wa ‘yan sanda cewa mijinta kan yi amfani da bindigar wajen razanar da ita, ‘ya’yansu da sauran mutane a unguwar.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Baba Mohammed Azare, ya ce rundunar za ta ci gaba da yaƙi da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba tare da tabbatar da cewa duk wanda ke amfani da makami wajen tada zaune tsaye zai fuskanci hukunci.
