Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta kama wani matashi mai shekaru 21, Samson Onilewaji, bayan an same shi da abin da ake zargin hannun mutum ne, tare da bindigogi da wasu kayayyakin da ake zargin an sace, yayin wani binciken ababen hawa a kan titin Lekki-Epe Expressway.
Kakakin rundunar, CSP Abimbola Adebisi, ta bayyana a wata sanarwa cewa jami’an ‘yan sanda sun tare wata motar haya marar lambar rajista da ke ɗauke da mutane shida a lokacin gudanar da binciken tsaro na yau da kullum.
A yayin binciken, an gano cewa Samson Onilewaji na ɗauke da abin da ake zargin hannun daman mutum ne, bindigogi biyu ƙirar gida, harsashi guda, gatari biyu, na’urar POS guda da katunan ATM guda biyar.
Bayan kama shi, wanda ake zargin ya amsa cewa kwanan nan ya yi wa mutum uku fashi tare da ƙwace musu kayayyakinsu, ciki har da na’urar POS da katunan ATM da aka samu a hannunsa.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano wanda hannun mutumin ya fito daga gare shi, yadda wanda ake zargin ya samu hannun da kuma abin da ya yi niyyar amfani da shi.
Haka kuma jami’an tsaro na ƙoƙarin gano tare da cafke sauran abokan aikinsa da ake zargin suna da hannu a ayyukan laifi.
Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, CP Tijani Olaiwola Fatai, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da manyan laifuka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya kuma yi kira ga al’umma da su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen hana aikata
