Gwamnatin Jihar Oyo ta ayyana ranar Talata, 16 ga Yunin 2026, a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Prince Dotun Oyelade, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin nuna girmamawa da haɗin kai da al’ummar Musulmi, yayin da ake tunawa da Hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.
Ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya.
Oyelade ya ƙara da cewa Hijrah lokaci ne na tunani, ibada da ƙarfafa zumunci tsakanin al’umma, yana mai kira ga jama’a da su yi koyi da darussan da ke cikin wannan babban tarihi na Musulunci.
