Kwamitin Raba Kudaden Tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.26 ga Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi a matsayin kudaden shiga na watan Afrilun 2026.
Adadin ya karu da Naira biliyan 217 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 2.04 da aka raba a watan da ya gabata, lamarin da ya nuna karin kudaden shiga da kashi 10.6 cikin dari.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Bawa Mokwa, ya fitar ta bayyana cewa kudaden da aka raba sun kunshi kudaden haraji na doka, kudaden VAT da kuma karin tallafin Naira biliyan 250.
Bayanan sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 787.35, yayin da jihohi suka samu Naira biliyan 772.36. Kananan hukumomi kuwa sun karbi Naira biliyan 540.15, yayin da jihohin da ake hako mai suka raba Naira biliyan 157.25 a matsayin kudin derivation.
FAAC ta bayyana cewa karuwar kudaden shiga ta samo asali ne daga karin kudaden Harajin Kamfanoni (CIT), VAT, kudin shigo da kaya da kuma kudaden sarauta daga bangaren mai da iskar gas.
Sai dai an samu raguwar kudaden Harajin Ribar Man Fetur (PPT) da kuma Hydrocarbon Tax, amma karin kudaden da aka samu daga wasu bangarori ya taimaka wajen kara yawan kudaden da aka raba.
Masana na ganin wannan karin kudade zai taimaka wa gwamnatoci wajen gudanar da ayyukan raya kasa, samar da ababen more rayuwa da kuma inganta ayyukan jin dadin al’umma a fadin Najeriya.
