Emmanuel Kanu ya bayyana cewa Nnamdi Kanu na kalubalantar hukuncin da aka yanke masa kan zargin ta’addanci, yana mai cewa an gina shari’ar ne bisa dokar da aka soke tun bayan fara aiki da sabuwar dokar ta’addanci ta shekarar 2022.
Ya ce Kanu ya sha neman kotu ta bayyana takamaiman dokar da aka same shi da laifi a karkashinta, yana mai jaddada cewa batun zai kasance muhimmin bangare na karar daukaka kara da aka shigar domin tantance ko hukuncin ya cika sharuddan kundin tsarin mulkin Najeriya.
