Hukumar Kula da Kare Bayanai ta Najeriya (NDPC) ta kaddamar da wani shiri na shekaru biyu tare da kamfanin Meta Platforms, wanda shi ne mamallakin Facebook, domin karfafa tsaro da kariyar bayanan sirri, horar da ma’aikata da kuma tabbatar da bin ka’idojin kare bayanai.
Wannan shiri mai suna Meta-Supported Initiatives for Data Protection (M-SIDP) ya biyo bayan tattaunawa tsakanin NDPC da Meta, bayan binciken da aka gudanar kan yadda kamfanin ke sarrafa bayanan masu amfani a Najeriya.
An kammala batun ne a shekarar 2025 ta hanyar wata yarjejeniya da kotu ta amince da ita, inda Meta ta amince da tallafawa shirye-shiryen wayar da kai da suka shafi kare bayanan jama’a.
A cikin sanarwar da Hukumar NDPC ta fitar, ta ce shirin zai gudana na tsawon shekaru biyu kuma zai mayar da hankali kan muhimman fannoni guda huɗu da suka hada da shugabanci da bincike, inganta tsaro a fannin fasaha, horar da jami’an kare bayanai, da kuma wayar da kan jama’a musamman masu rauni a cikin al’umma.
Hukumar ta ce wannan shiri ba zai hana ta ci gaba da aikinta na doka ba, domin za ta ci gaba da sa ido kan yadda ake sarrafa bayanan mutane a Najeriya bisa dokokin da ke akwai.
NDPC ta kuma bayyana cewa tana da burin inganta amincewar jama’a ga tsarin dijital tare da jawo jarin kamfanoni a fannin fasaha.
A bangaren Meta, shirin na nuna sabon mataki na kyautata dangantaka da hukumomin Najeriya, bayan takaddama da ta shafi yadda ake kula da bayanan masu amfani da kafafen sada zumunta a kasar.
