Wata kungiyar magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai suna Relax Tinubu Is Fixing Nigeria (RTIFN) ta kaddamar da shirin rajistar mambobi a fadin kasar nan da nufin tattara masu kada kuri’a miliyan 5.25 gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Shirin rajistar na kwanaki 30 ya fara ne daga ranar 1 ga watan Yuni kuma zai kare a ranar 30 ga watan Yuni. Ana sa ran matasa, mata, kwararru, kungiyoyin kasuwanni, ma’aikatan sufuri, masu bukata ta musamman, shugabannin al’umma da sauran ‘yan Najeriya ciki da wajen kasar su shiga cikin shirin.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, Darakta Janar na RTIFN, Hon. Ahmed Bala, ya ce an kirkiro wannan shiri ne domin kara karfafa goyon baya ga manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da fadada shiga cikin harkokin mulki a matakin kasa.
Ya bayyana rajistar a matsayin kira ga duk ‘yan Najeriya masu kishin ci gaban kasa, hadin kai, zaman lafiya, tsaro da bunkasar tattalin arziki.
Ahmed Bala ya ce kungiyar na ci gaba da goyon bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu, yana mai kira ga ‘yan kasa da su ci gaba da kasancewa masu fata duk da kalubalen da ake fuskanta.
A cewarsa, rajistar a bude take ga mambobin APC da wadanda ba mambobi ba, domin gina babban sansanin masu goyon bayan Shugaban kasa kafin babban zaben 2027.
Ya kuma yaba wa wanda ya kafa kungiyar, Mista Seyi Tinubu, bisa kokarinsa wajen bunkasa matasa da ba su damar shiga harkokin ci gaba.
Sakataren kungiyar na kasa, Felix Arome, ya ce za a gudanar da rajistar ta yanar gizo da kuma a cibiyoyin rajista na zahiri.
Ya bayyana cewa tsarin na yanar gizo zai taimaka wajen gina cikakken bayanan mambobi, bibiyar masu kada kuri’a da kuma yada manufofin gwamnati ga masu goyon baya. Haka kuma ya ce ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje za su iya shiga cikin tsarin.
Shi ma mai kula da yankin Kudu maso Gabas na kungiyar, High Chief Engr. Johnbosco Onunkwo, ya ce kungiyar ta rungumi amfani da fasahar zamani domin fadada tasirinta a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa manufar ba wai kawai gabatar da manufofin Tinubu ga jama’a ba ce, har ma da gamsar da su kan hangen nesan shugabancinsa.
Jagorar Mata ta Kasa na kungiyar, Dr. Umma Adamu Sani, ta tabbatar da cewa mata za su taka muhimmiyar rawa wajen wannan gangamin wayar da kai, ta hanyar kai sakon kungiyar zuwa matakin al’umma.
A nasa bangaren, Daraktan Hulda da Tattara Magoya Baya na kungiyar, Mista Lulu Fawehinmi, ya ce suna sa ran samun akalla kuri’u miliyan biyar ta hanyar wannan shiri.
Ya bayyana cewa za a iya yin rajista ta yanar gizo ko kuma a cibiyoyin da aka tanada a mazabu, kananan hukumomi, jihohi, kasuwanni da cibiyoyin al’umma a fadin kasar.
Fawehinmi ya kara da cewa mambobin da suka yi rajista za su amfana da shiga shirye-shiryen kungiyar, ayyukan sa-kai, samun bayanan manufofi da kuma ayyukan ci gaban al’umma.
