Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yabawa tsohon shugaban mulkin soja, Yakubu Gowon, bisa rawar da ya taka wajen haɗa kan Najeriya bayan yaƙin basasa, yana mai cewa furucin “ba mai nasara, ba wanda aka ci” ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar.
Jonathan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da tarihin rayuwar Gowon, inda ya ce littafin ya nuna irin shugabanci, kishin ƙasa da ƙoƙarin gina Najeriya da tsohon shugaban ya yi.
Ya ce lokacin yaƙin basasa daga shekarar 1967 zuwa 1970 na daga cikin mafi wahalar lokuta a tarihin Najeriya, amma Gowon ya nuna dattako da hangen nesa bayan yaƙin ta hanyar rungumar sulhu da sake haɗa kan al’umma.
A cewarsa, matakin “ba mai nasara, ba wanda aka ci” ya taimaka wajen warkar da raunukan yaƙi da dawo da haɗin kai tsakanin ‘yan Najeriya.
Jonathan ya kuma yabawa Gowon kan kafa shirin bautar ƙasa na NYSC, yana mai cewa tsarin ya taimaka wajen haɗa matasa daga sassa daban-daban na ƙasar tare da magance ƙarancin malamai a wasu makarantu a wancan lokaci.
Ya tuna cewa wasu matasan NYSC da aka tura makarantar da yake karatu sun taimaka masa sosai wajen koyon darussa kamar Lissafi, Chemistry da Biology.
Tsohon shugaban ya ƙara da cewa Gowon ya ci gaba da bayar da gudummawa wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban matasa tun bayan barinsa mulki.
Jonathan ya jaddada cewa irin waɗannan tarihin rayuwa suna da muhimmanci wajen koyar da matasa tarihin Najeriya da fahimtar nauyin shugabanci a lokutan ƙa0lubale.
