Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta naɗa tsohon gwamnan Jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke, da tsohon gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, domin jagorantar manyan kwamitocin gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa gabanin zaɓen cikin gida na jam’iyyar.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Imoke zai jagoranci Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa, yayin da Ahmed zai kasance shugaban Kwamitin Gudanar da Zaɓen Fidda Gwanin Shugaban Ƙasa.
Kwamitin tantancewar ya ƙunshi manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da Hon. C.I.D. Maduabum a matsayin sakatare, tare da wasu mambobi da suka fito daga sassa daban-daban na ƙasar.
Haka kuma, kwamitin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ya haɗa da fitattun mutane da dama domin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zaɓen.
Jam’iyyar ta kuma kafa Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na shugaban ƙasa, wanda zai kula da duk wani ƙorafi da zai taso yayin gudanar da zaɓen fidda gwani.
Baya ga hakan, ADC ta kafa kwamitoci daban-daban domin tantance ‘yan takarar gwamna da kuma sauraron ƙorafe-ƙorafe a jihohi.
Jam’iyyar ta ce an tsara dukkan waɗannan kwamitoci ne domin tabbatar da gaskiya, adalci, sahihanci da ingantaccen dimokuraɗiyya a dukkan matakan zaɓen fidda gwani nata.
