Shahararren ɗan damben nan na Birtaniya, Anthony Joshua, na shirin dawowa fagen dambe a ranar 25 ga watan Yuli, inda zai fafata da ɗan damben Albania, Kristian Prenga, a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.
Wannan fafatawar za ta zama tamkar gwaji ne kafin babbar arangama da ake jira tsakaninsa da Tyson Fury a ƙarshen shekara.
Shugaban harkokin dambe na Saudiyya, Turki Alalshikh, ne ya bayyana hakan, inda ya ce za a gudanar da wasan a cikin wani babban shiri da ake kira “Esports World Cup”, kuma za a watsa shi kai tsaye ta tashar DAZN.
Wannan ne karon farko da Joshua zai koma ring bayan nasarar da ya samu a kan Jake Paul a watan Disamba.
Bayan wannan nasara, Joshua ya fuskanci wani mummunan haɗarin mota a Najeriya wanda ya yi sanadin mutuwar wasu abokansa guda biyu, yayin da shi kuma ya samu ƙananan raunuka. Sai dai tun daga lokacin ya koma atisaye domin shirye-shiryen dawowa fagen.
Joshua ya bayyana cewa ya ɗauki lokaci ne domin gyara jikinsa da kuma shirya kansa kafin komawa fafatawa.
“Na ɗauki lokaci domin sake ginawa da kuma shiri. Wannan mataki ne na gaba a tafiyata,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa ya rattaba hannu kan yarjejeniyar wasanni biyu a Saudiyya, wanda zai kai shi zuwa babban fafatawa da Fury daga baya.
Idan Joshua ya yi nasara a kan Prenga, hakan zai share masa hanya zuwa babbar arangama da Fury, wadda magoya baya ke jira tun shekaru.
