Kalu ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a harabar Majalisar Tarayya a Abuja, yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 66.
Ya bayyana zargin da wasu jam’iyyun adawa, ciki har da African Democratic Congress (ADC), ke yi a matsayin mara tushe kuma mai rage martabar dimokuradiyya a Najeriya.
A cewarsa:
“APC ba ta da wata alaƙa da INEC. INEC hukuma ce mai zaman kanta, kuma muna mutunta shugabancinta. Jama’a su daina wannan magana mara tushe,” in ji shi.
KAN ZARGIN SHIGA JAM’IYYA DA KARFI
Sanatan ya kuma musanta zargin cewa APC na matsa lamba ga ‘yan siyasa, musamman gwamnoni, su koma jam’iyyar.
Ya ce shigar jam’iyya abu ne na son rai, ba tilas ba.
“Shugaba Tinubu bai taba tilasta wa kowa shiga jam’iyyarmu ba. Idan gwamna ya yanke shawarar shiga APC, hakan nasa ne,” in ji Kalu.
HASASHEN ZABEN 2027
Dangane da jita-jitar rabon mukaman siyasa kafin zaben 2027, Kalu ya ce bai san wani tsari na irin haka ba, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa suna hannun shugabannin jam’iyya ne.
Ya kuma ce ba ya neman wani mukami a yanzu, duk da cewa ba ya hana yiwuwar siyasa a gaba.
CI GABAN KASA DA ZARGI
Kalu ya kuma yi watsi da korafe-korafen wasu tsofaffin gwamnoni na 1999 kan wariya, yana mai cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da kyakkyawar hulda da tsofaffin shugabanni.
KAN CI GABAN YANKI
Ya ce bai dace a ce an ware Kudu maso Gabas ba, yana mai cewa dukkan shugabanni tun da da suka wuce suna ba da gudummawa wajen ci gaban kasa.
“Buhari ya yi nasa, Tinubu ma yana yi. Ana samun ci gaba a duk fadin kasa,” in ji shi.
KAN TATTALIN ARZIKI
Sanatan ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arziki na gwamnati na nuna sakamako a sama, amma har yanzu akwai matsaloli a kasa saboda rashin tsaro da wasu kalubale.
HASASHEN ZABEN 2027
Kalu ya bayyana kwarin gwiwa cewa Shugaba Tinubu zai lashe zaben 2027, yana mai cewa APC na kara karfi a fadin kasa.
“Ban ga wanda zai kayar da Tinubu a zabe na gaskiya ba. APC tana tafiya kamar jirgin kasa mai karfi,” in ji shi.
