Mai kula da ayyukan agajin gaggawa na United Nations, Tom Fletcher, ya ware dala miliyan 48 daga asusun UN Central Emergency Response Fund domin tallafawa ayyukan UN Humanitarian Air Service.
Sabon tallafin zai taimaka wajen ci gaba da ayyukan jiragen agaji na UNHAS a ƙasashe takwas da suka haɗa da Nigeria, Chad, Democratic Republic of the Congo, Haiti, Kenya, South Sudan, Sudan da kuma Syria.
Wannan mataki zai bai wa dubban ma’aikatan agaji daga Majalisar Dinkin Duniya, kungiyoyin sa-kai (NGOs) da sauran ƙungiyoyin al’umma damar ci gaba da ayyukansu na kai taimako ga masu bukata.
Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar MDD da ke New York cewa UNHAS na taka muhimmiyar rawa wajen kai ma’aikatan agaji da kayan taimako zuwa wuraren da ake bukata, kamar yadda World Food Programme ya bayyana.
Sai dai ya yi gargadin cewa, sakamakon raguwar kuɗaɗen agaji a duniya, akwai yiwuwar a dakatar da wasu jiragen UNHAS idan ba a samu ƙarin tallafi ba.
