Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya mayar da martani ga mawakin Najeriya Davido kan kiransa da ya tabbatar da zaman lafiya a gabanin zaɓen gwamnan Jihar Osun na ranar 15 ga Agusta, 2026.
Ko da yake Davido bai ambaci sunan Uzodimma kai tsaye ba, ya buƙaci shugabannin siyasa su tabbatar da zaman lafiya tare da barin al’ummar Osun su zaɓi ɗan takarar da suke so ba tare da tsangwama ba.
Sai dai a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Kafafen Sadarwa, Ambrose Nwaogwugwu, ya fitar, Uzodimma ya ce ya kamata Davido ya mayar da hankalinsa wajen yin kira ga masu zaɓe a Osun maimakon yi masa kira.
Gwamnan ya kuma yi hasashen cewa Gwamna Ademola Adeleke, wanda ke neman wa’adi na biyu, zai sha kaye a zaɓen, yana mai cewa mutane da dama sun rasa amincewa da salon mulkinsa.
A cewar sanarwar, alamu daga sassa daban-daban na jihar Osun na nuna cewa masu zaɓe da yawa sun shirya goyon bayan ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen.
Uzodimma ya kuma shawarci Davido da ya fara shirya kawunsa, Gwamna Adeleke, domin rayuwa bayan barin mulki maimakon yin kira na tausayi ga shugabannin siyasa.
A wani ɓangare na sanarwar, gwamnan ya yi barkwanci da cewa idan Adeleke ya fice daga mulki, watakila Davido zai iya ɗaukarsa aiki a matsayin ɗan rawa a ƙungiyar mawakansa.
Wannan musayar kalamai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen gwamnan Jihar Osun, inda Gwamna Ademola Adeleke ke neman sake komawa kan kujerarsa.
