An ci gaba da gudanar da bukukuwa da kuma aika saƙonnin taya murna ga Archbishop Margaret Benson-Idahosa, shugabar Church of God Mission International, yayin da ta cika shekaru 83 a duniya.
Bikin, wanda ya ɗauki kusan mako guda, ya haɗa iyalanta, ‘ya’yanta na ruhaniya, limamai, jami’an gwamnati da sauran masoya daga sassa daban-daban na duniya, inda suka yi mata fatan alheri tare da yabawa irin gudunmawar da ta bayar ga addini da al’umma.
An fara bikin ne da saƙonnin taya murna daga ‘ya’yanta, sannan fastoci, ‘yan uwa da abokan arziki daga ƙasashe daban-daban suka ci gaba da aika mata da addu’o’i da kalaman yabo.
A wani saƙo da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ɗiyarta Rantiade ta bayyana mahaifiyarta a matsayin uwa ta musamman, jagorar al’umma kuma ginshiƙin ƙarfi ga iyalanta da mabiyanta.
Ta kuma wallafa takaitaccen tarihin rayuwar Archbishop Margaret Benson-Idahosa, inda ta yaba da jajircewarta, bangaskiyarta da kuma irin ƙarfin halinta, musamman bayan rasuwar mijinta, marigayi Archbishop Benson Idahosa.
Masu taya ta murna sun bayyana cewa rayuwar Archbishop Margaret Benson-Idahosa ta kasance abin koyi ga miliyoyin mabiya addinin Kirista a Najeriya da ma duniya baki ɗaya
