Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) reshen Jihar Kebbi ta yi zargin cewa gurfanar da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a gaban kotu na da nasaba da siyasa, domin raunana ‘yan adawa kafin babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ADC na jihar, Engr. Sufiyanu Bala, da Shugaban Majalisar Dattawan jam’iyyar, Alhaji Shehu Aliyu Sambawa, suka sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ba ta adawa da bincike ko gurfanar da kowa idan akwai hujjoji, amma ta yi ikirarin cewa yadda aka gudanar da lamarin ya nuna alamun tsangwama ta siyasa.
ADC ta kuma yi zargin cewa kama da tsare Malami, da binciken gidajensa tare da bayyana kadarorinsa a bainar jama’a, an yi su ne domin bata masa suna.
Jam’iyyar ta zargi jam’iyyar APC da amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da wasu sassan tsarin shari’a wajen matsa wa ‘yan adawa lamba kafin zaɓen 2027.
Sai dai har yanzu, babu wata hujja da kotu ta tabbatar da ke nuna cewa zarge-zargen na da alaƙa da siyasa, kuma ana sa ran shari’ar za ta ci gaba a gaban kotu.
