Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce ba ya samun karbuwa a wajen ma’aikatan gwamnati da dama saboda matakan da ya dauka na dakile almubazzaranci da karkatar da kudaden gwamnati.
Da yake jawabi a taron tattaunawa da manema labarai na wata-wata a Abuja, Wike ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ayyukan raya kasa maimakon kashe kudade kan tafiye-tafiye da tarukan da ba su da amfani.
Ya ce ba zai amince a kashe miliyoyin naira wajen tura jami’an gwamnati kasashen waje domin halartar taruka ba, alhali za su iya koyon irin wadannan abubuwa a cikin Najeriya.
A cewarsa, kafin ya karbi ragamar jagorancin FCT, kusan kashi 65 cikin 100 na kasafin kudin babban birnin na tafiya ne wajen biyan kudaden gudanarwa, yayin da ayyukan raya kasa ke samun kaso kadan.
Wike ya ce ya sauya tsarin ta hanyar ware kashi 70 cikin 100 na kasafin kudi domin ayyukan ci gaba, sannan kashi 30 cikin 100 kacal ya rage wa kudaden gudanarwa.
Ya kuma yi zargin cewa wasu tarukan gwamnati sun zama hanyoyin karkatar da kudaden jama’a maimakon inganta aikin gwamnati.
Ministan ya ce kudaden da ake kashewa kan irin wadannan taruka yanzu ana amfani da su wajen gina tituna da sauran muhimman ayyukan more rayuwa, yana mai cewa hakan ne ya sa wasu ma’aikatan gwamnati ba sa jin dadinsa.
