Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Benue ta kama wani matashi mai shekaru 23 mai suna Abdullahi Usman bisa zarginsa da hannu a kisan wani malami a Jami’ar Jihar Benue, Farfesa Gabriel Saawua Nyityo.
Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa jami’an ‘yan sanda sun samu kiran gaggawa daga yankin Adaka da ke Makurdi, inda suka tarar da gawarwakin mutum biyu.
A cewar rundunar, wadanda aka kashe sun hada da Farfesa Gabriel Nyityo mai shekaru 58 da kuma kanensa, Iorngee John Nyityo mai shekaru 19.
Sanarwar ta ce an kama Abdullahi Usman, dan asalin karamar hukumar Awe a Jihar Nasarawa, dangane da wannan kisa, yayin da ake ci gaba da bincike domin cafke sauran wadanda ake zargi da hannu a harin.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe Farfesan da kanensa ne a gidansu da ke unguwar Adaka a karamar hukumar Makurdi cikin safiyar ranar Laraba.
Kisan ya jefa al’ummar yankin Adaka da kuma jami’ar cikin jimami, duk da cewa malamai a Jami’ar Jihar Benue na ci gaba da yajin aiki a halin yanzu.
