Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince da nadin Lamido Yuguda Abubakar a matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Kula da Kadarorin Bankuna ta Kasa (AMCON).
Bukatar na kunshe ne cikin wata wasika da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Laraba.
A cikin wasikar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa an gabatar da nadin ne bisa tanadin dokar kafa AMCON ta shekarar 2019 da aka yi wa kwaskwarima.
Ya ce an zabi Lamido Yuguda ne domin maye gurbin tsohon shugaban kwamitin gudanarwar hukumar da ya bar mukaminsa.
Shugaban ya kuma bukaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance tare da amincewa da nadin domin ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar yadda ya kamata.
Bayan karanta wasikar, Shugaban Majalisar Dattawa ya mika batun ga Kwamitin Majalisar kan Harkokin Bankuna, Inshora da Sauran Hukumomin Kudi domin tantance wanda aka nada tare da gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.
An kafa AMCON ne a shekarar 2010 domin taimakawa wajen daidaita tsarin harkokin kudi na Najeriya ta hanyar karbar basussukan da suka zama matsala daga bankuna da kuma kokarin karbo bashin da ake bin su.
