Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na bai wa matasa dama da kuma karfafa musu gwiwa, inda ya amince da shirya Taron Tsaron Matasa na Jihar Kogi domin kara inganta tsaro da ci gaba mai dorewa a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin shugabannin matasa da sauran masu ruwa da tsaki a Fadar Gwamnati da ke Lokoja.
Ododo ya ce matasa su ne ginshikin al’umma, kuma suna da kuzari, basira da kwarewar da za su taimaka wajen gina makomar jihar idan aka ba su dama.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sanya matasa a tsakiyar tafiyar da mulki ta hanyar samar da manufofi da ke ba su damar shiga cikin yanke shawara da aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.
A cewarsa, Taron Tsaron Matasa na Kogi zai zama wata kafa da za ta hada matasa, gwamnati da hukumomin tsaro domin samar da mafita ga matsalolin tsaro da sauran ayyukan laifi a jihar.
Gwamnan ya kuma tabbatar da goyon bayansa ga aikin gina Ododo Youth House, yana mai cewa za a aiwatar da shi ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP), domin tabbatar da dorewarsa.
Ya ce cibiyar za ta kasance wurin bunkasa kirkire-kirkire, horas da shugabanci da koyar da sana’o’i, tare da babban dakin taro mai daukar mutane 1,000, ofisoshi, dakin karatu, wurin shakatawar yara da sauran kayayyakin more rayuwa.
Ododo ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kara tallafin da ake bai wa reshen Kungiyar Matasan Najeriya (NYCN) na Jihar Kogi duk wata, wanda ya shafe sama da shekara goma yana kan naira dubu 500.
Haka kuma ya yi alkawarin gudanar da tarurruka da kungiyoyin matasa duk bayan watanni uku domin karfafa hadin kai da sauraron bukatunsu.
Tun da farko, Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Monday Anyebe, ya yabawa gwamnatin Ododo, yana mai cewa ta nuna cikakken goyon baya ga matasa ta hanyar ba su manyan mukamai a majalisar zartarwar jihar.
Shi ma Shugaban NYCN na Jihar Kogi, Kwamared Abdurrahman Abdulmumin Enesi, ya yaba wa gwamnan bisa fifita ci gaban matasa da kuma shigar da su cikin harkokin mulki.
Enesi ya bukaci gwamnan ya kara nada matasa masu kwarewa a manyan mukaman gwamnati, sannan ya roki a kara tallafin kungiyar daga naira dubu 500 zuwa naira miliyan biyar a duk wata domin fadada shirye-shiryen da za su amfani matasan jihar.
Ya ce amincewar gwamnan da shirya Taron Tsaron Matasa da sauran shirye-shiryen bunkasa matasa ya nuna kudirin gwamnatin na sanya matasa a gaba wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban Jihar Kogi.
