Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen yankin Ibadan, ta bukaci Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da takwaransa na Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da su fara cikakken aiwatar da yarjejeniyar FGN-ASUU ta shekarar 2025 daga watan Yulin 2026.
ASUU ta bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Jami’ar Emmanuel Alayande University of Education da ke Oyo, inda ta ce rashin aiwatar da yarjejeniyar na jefa rayuwar mambobinta cikin mawuyacin hali sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar.
Taron ya haɗa da rassan ASUU na Jami’ar Ibadan, Jami’ar Ilorin, LAUTECH Ogbomoso, Jami’ar Jihar Osun, Jami’ar Jihar Kwara da kuma Emmanuel Alayande University of Education.
Kungiyar ta yabawa majalisun gudanarwar jami’o’in jihohin saboda ƙoƙarin da suke yi wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar, amma ta zargi gwamnonin Oyo da Kwara da gaza samar da kuɗaɗen da ake buƙata domin cika alkawuran da aka ɗauka.
ASUU ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin adalci ga malaman jami’o’in.
Da yake jawabi a madadin kungiyar, Kodinetan ASUU na yankin Ibadan, Farfesa Biodun Olaniran, ya ce haƙurin mambobin kungiyar ya ƙare, saboda haka sun fara shirye-shiryen shiga cikakken yajin aikin sai baba-ta-gani idan gwamnatocin jihohin suka ci gaba da kin aiwatar da yarjejeniyar.
Kungiyar ta buƙaci cewa albashin watan Yuli ya ƙunshi CATA da duk wasu alawus-alawus da ke cikin yarjejeniyar, tare da biyan dukkan bashin da ya taru tun daga watan Janairun 2026.
ASUU ta yi gargadin cewa duk wani jinkiri ko gazawa daga gwamnatocin jihohin zai tilasta mata shiga yajin aikin da ba a sanya ranar ƙarewa ba.
Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnonin Oyo da Kwara da su ɗauki matakin gaggawa kafin jami’o’in su rufe saboda yajin aiki, tana mai jaddada cewa cikakken aiwatar da yarjejeniyar shi ne hanya mafi dacewa wajen tabbatar da zaman lafiya a jami’o’in.
A ƙarshe, ASUU ta jajanta wa gwamnatin Jihar Oyo da iyalan waɗanda matsalar tsaro ta shafa, tare da kira ga gwamnati da ta ƙara inganta tsarin tsaro domin samar da yanayin zaman lafiya da ilimi zai bunƙasa.
