Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Anambra ta tabbatar da kama mutumin da ya ɗauki tare da yaɗa wani bidiyo a kafafen sada zumunta, inda ya yi ikirarin cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu ya sauke wasu kayayyaki da ba a san ko mene ne ba a wani daji tsakanin al’ummomin Nimo da Adazi-Nnukwu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya ce bincike ya nuna cewa mutumin ya ɗauki bidiyon ne daga wani gida da ke kusa da CKP, ba daga wurin da ya yi ikirarin lamarin ya faru ba.
Ikenga ya ce wanda ake zargin ya amsa yayin tambayoyi cewa bai ga wani jirgin sama ya sauka ba, kuma ya ƙirƙiri labarin ne bisa jita-jitar da ya ji daga wasu mutane.
Ya ce shugaban al’ummar yankin tare da jami’an tsaro sun zagaya yankin da garuruwan da ke makwabtaka domin tabbatar da gaskiyar lamarin, kuma duk mutanen da suka tattauna da su sun tabbatar da cewa babu wani jirgin sama da ya sauka ko ya yi shawagi a yankin Okudugbo.
A cewarsa, jirgin sama mai saukar ungulu ya wuce ne kawai sama da yankin kamar yadda ya saba yi a wasu lokuta, amma wanda ake zargin ya yi amfani da wannan damar wajen ƙirƙirar labari mai tayar da hankali domin samun farin jini a kafafen sada zumunta.
Ikenga ya ce za a miƙa wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) domin ci gaba da bincike kan zargin yaɗa ƙarya da kuma haddasa fargaba a tsakanin al’umma.
Ya ƙara da cewa shugabannin al’ummomin da ke makwabtaka sun nuna rashin jin daɗinsu kan firgicin da bidiyon ya jawo.
Rundunar ta buƙaci jama’a su kasance masu sa ido kan harkokin tsaro tare da kai rahoton duk wani abu da suka gani mai tayar da hankali ga hukumomin da abin ya shafa, amma su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su domin kauce wa haddasa firgici.
A baya dai rundunar ‘yan sandan Anambra ta musanta rahotannin da suka bazu a kafafen sada zumunta cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu ya sauke wasu kayayyaki a cikin daji tsakanin Nimo da Adazi-Nnukwu, tana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da ke iya haddasa tashin hankali da firgici a tsakanin jama’a.
