Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da sanya kansu a matsayin jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) domin gudanar da ayyukan da ba su da izini da kuma karbar kudade daga jama’a.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Maureen Chinaka, ta bayyana cewa binciken farko ya nuna wadanda ake zargin mambobi ne na wata kungiya mai suna Social Watch Anti-Drugs Abuse Advocacy, wadda aka kafa domin wayar da kan jama’a kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Sai dai ta ce ana zargin sun yi amfani da sunan kungiyar a matsayin kariya wajen kwaikwayon jami’an NDLEA tare da gudanar da ayyukan kama mutane ba bisa ka’ida ba a cikin garin Umuahia.
A cewarta, an kama mutanen ne bayan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta wanda ya nuna wasu mutane biyu, daya sanye da kayan jami’an tsaro na al’umma, suna dukan wani direban adaidaita sahu tare da sanya masa ankwa.
Chinaka ta kara da cewa ana zargin mutanen da kama jama’a ba bisa doka ba da kuma karbar kudade daga hannunsu da sunan yaki da miyagun kwayoyi.
Ta bayyana cewa bincike mai zurfi na ci gaba domin tabbatar da gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin zama izina ga sauran masu irin wannan dabi’a.
Shi ma Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Danladi Isa, ya gargadi jama’a da kada su dauki doka a hannunsu.
Ya ce duk da cewa dokar ACJA ta ba fararen hula damar kama wanda suka gani yana aikata laifi, wajibi ne a mika irin wannan mutum ga jami’an tsaro cikin gaggawa.
Kwamishinan ya jaddada cewa amfani da karfi, duka, tsoratarwa ko kuma kwaikwayon jami’an tsaro domin karbar kudade daga jama’a laifi ne da ba za a lamunta da shi ba.
Rundunar ta kuma bukaci mazauna jihar da su rika kai rahoton duk wani motsi ko aiki da suke zargin ba bisa ka’ida ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko lambobin gaggawa da aka tanada.
Lamarin ya sake nuna yadda wasu masu aikata laifuka ke amfani da sunayen hukumomin tsaro wajen yaudarar jama’a da kuma cin zarafinsu.
