Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar a saki fitaccen dan gwagwarmaya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, , zuwa hannun lauyoyinsa har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatarsa.
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyoyin Sowore sun sanar da kotun cewa sun shigar da bukatar soke umarnin da kotun ta bayar a ranar 16 ga Yuni wanda ya janye belinsa tare da bayar da sammacin kama shi.
Lauyoyin sun bukaci kotun da ta dawo da tsoffin sharuddan belin Sowore tare da soke duk wasu matakan da aka dauka a kansa.
Sai dai bangaren gwamnatin tarayya ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar, yana mai cewa wanda ake kara bai gabatar da hujjojin da za su sa kotun ta yi amfani da ikonta a kansa ba.
Bayan sauraron bangarorin biyu, Mai Shari’a Mohammed Umar ya dage yanke hukunci kan bukatar zuwa ranar 30 ga Yuni, 2026.
Bayan dage zaman, bangaren kare Sowore ya sake rokon kotun da ta saki wanda ake kara zuwa hannun lauyoyinsa har zuwa ranar yanke hukuncin, tare da yin alkawarin dawo da shi kotu idan an bukata.
Sai dai lauyan gwamnati ya yi adawa da bukatar, yana mai cewa ya kamata a gabatar da ita a rubuce domin bangaren gwamnati ya samu damar mayar da martani.
Lauyoyin Sowore sun kuma bayyana wa kotun cewa sun samu bayanin cewa lafiyarsa ba ta da kyau, don haka suka nemi a amince da bukatar.
Duk da haka, Mai Shari’a Umar ya ce amincewa da bukatar zai saba da manufar dage karar domin shirya hukunci, musamman ganin cewa har yanzu bai kammala nazarin dukkan takardun da bangarorin suka gabatar ba.
Saboda haka, kotun ta yi watsi da bukatar tare da umartar a mayar da Sowore gidan yari har zuwa ranar 30 ga Yuni, lokacin da za a yanke hukunci kan bukatarsa.
Sowore dai ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, kuma ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin mara laifi.
