Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, , ya yi kira ga sanatoci da su tabbatar sun halarci zaman majalisar na ranar Laraba domin tattaunawa da kada kuri’a kan kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya.
Da yake jawabi a zaman majalisar na ranar Talata, Akpabio ya bayyana kudirin a matsayin wani muhimmin mataki da zai sauya tsarin tsaron Najeriya tare da taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da ke kara yawaita a sassan kasar.
Ya ce tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, Najeriya ba ta samu damar raba harkar ‘yan sanda zuwa matakin jihohi ba, yana mai cewa yanzu lokaci ya yi da za a dauki wannan mataki domin inganta tsaro.
Akpabio ya tunatar da sanatocin cewa gyaran kundin tsarin mulki na bukatar goyon bayan mafi rinjayen ‘yan majalisa, saboda haka ya bukace su da su dauki lamarin a matsayin nauyin kasa baki daya.
A cewarsa, kafa ‘yan sandan jihohi zai bai wa kananan hukumomi, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da kungiyoyin matasa damar taka rawa sosai wajen samar da bayanan sirri da kuma tabbatar da tsaro a yankunansu.
Shugaban Majalisar ya kuma umurci Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki da ya gabatar da rahotonsa kan kudirin a ranar Laraba, 24 ga Yunin 2026, domin a fara daukar matakan doka cikin gaggawa.
Shi ma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, , ya jaddada muhimmancin halartar zaman, yana mai cewa ana bukatar akalla kashi biyu bisa uku na sanatoci domin amincewa da duk wani gyaran kundin tsarin mulki.
Ya bayyana kudirin kafa ‘yan sandan jihohi a matsayin batu na kasa wanda ya wuce siyasa, yanki ko bambancin jam’iyyu, tare da kira ga dukkan sanatoci su halarci zaman domin yanke hukunci kan daya daga cikin manyan sauye-sauyen tsarin tsaro a tarihin dimokuradiyyar Najeriya.
Majalisar Dattawa ta dage zamanta zuwa ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026, inda ake sa ran za a gudanar da muhawara tare da kada kuri’a kan kudirin.
