Iyaye da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a jihar Oyo sun bayyana damuwa matuka kan illar da yajin aikin da kungiyar Malaman Najeriya (NUT) reshen jihar ke yi ke haifarwa ga dubban dalibai da yara masu karatu a fadin jihar.
Yajin aikin, wanda ya fara ne tun ranar 1 ga watan Yuni, ya biyo bayan sace wasu malamai da dalibai a karamar hukumar Oriire a ranar 15 ga watan Mayu. Tun daga lokacin, makarantun firamare da sakandare na gwamnati suka kasance a rufe, lamarin da ya katse harkokin karatu tare da barin yara da dama a gida ba tare da wani tsari na ilmantarwa ba.
Wasu iyaye da malamai da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) sun bayyana cewa tsawaita yajin aikin na kara jefa yara cikin zaman banza, yayin da wasu ke yawo a tituna ko kuma shiga wasu ayyukan da ka iya kawo cikas ga tarbiyyarsu da makomarsu.
Wata malama mai suna Yemisi Alao ta ce rashin kulawar wasu iyaye ga yaransu a wannan lokaci abin damuwa ne, inda ta yi zargin cewa wasu iyaye na fita wuraren aiki ko kasuwanci suna barin yaransu ba tare da kulawa ba.
Ta bayyana cewa hakan na iya haifar da matsaloli ga tarbiyyar yara, musamman idan aka yi la’akari da cewa suna cikin wani muhimmin mataki na shekarar karatu.
A cewarta, lokacin da makarantu za su koma aiki, malamai za su iya fuskantar matsin lamba wajen kokarin cike darussan da suka rasa saboda dogon lokacin da aka shafe ba a karatu ba.
Ta kuma yi kira ga al’umma da su taimaka wajen kula da yara ta hanyar karfafa musu gwiwa kan karatu, wasanni da sauran ayyukan da za su amfani kwakwalensu domin kaucewa fadawa cikin miyagun dabi’u.
Shi ma wani uba mai suna Godwin Obinna ya bayyana cewa yaransa na ta tambayarsa ko za su sake komawa makaranta, yana mai cewa lamarin ya fara damun su sosai.
Ya bukaci gwamnatin jihar Oyo da ta gaggauta magance matsalolin da suka haddasa yajin aikin tare da daukar matakan tsaro masu inganci a makarantu domin kare rayukan malamai da dalibai.
A wani bangaren kuma, wasu iyaye sun ce sun samar da hanyoyin kula da yaransu yayin da makarantu ke rufe. Wasu sun hada kai a unguwanni domin sanya ido kan yara, yayin da wasu kuma suka tura yaransu koyon sana’o’i domin kada su kasance cikin zaman banza.
Sai dai sun bayyana cewa yara kanana, musamman masu shekaru tsakanin uku zuwa bakwai, su ne suka fi fuskantar matsala saboda rashin samun damar shiga irin wadannan shirye-shirye na koyon sana’a.
Masu ruwa da tsaki a harkar ilimi sun yi gargadin cewa idan aka ci gaba da rufe makarantu na dogon lokaci, hakan na iya yin tasiri ga ci gaban karatu, tarbiyya da kuma makomar dubban yara a jihar.
A halin yanzu, iyaye da malamai na ci gaba da kira ga gwamnati da kungiyoyin da abin ya shafa da su nemo mafita cikin gaggawa domin yara su koma azuzuwansu, yayin da ake addu’ar ganin an kubutar da wadanda aka sace tare da dawo da zaman lafiya makarantu.
