Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, sun bukaci a kara amfani da fasahohin zamani tare da karfafa hadin gwiwar kasashen yankin domin inganta tsaron iyakokin Najeriya da dakile matsalolin tsaro da ke addabar kasar.
Sun bayyana hakan ne a taron karawa juna sani na kasa karo na 15 kan harkokin tsaro wanda Kungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Tsaro ta Kasa (AANDEC) ta shirya a Abuja.
Ribadu, wanda Daraktan Tsare-tsare da Manufofi na Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Yazid Gbemudu, ya wakilta, ya ce tsaron iyakokin kasa na da matukar muhimmanci wajen kare martabar Najeriya da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.
Ya bayyana cewa duk da irin gudunmawar da iyakokin Najeriya ke bayarwa wajen kasuwanci da hadin gwiwar yankuna, suna kuma fuskantar barazana daga ta’addanci, safarar makamai, fataucin bil’adama, shige da fice ba bisa ka’ida ba da sauran manyan laifukan kasa da kasa.
A cewarsa, gwamnatin tarayya na aiwatar da Tsarin Gudanar da Iyakoki na Kasa (National Border Management Strategy), wanda ke da nufin kara hadin gwiwar hukumomin tsaro, inganta kayan aikin sa ido da kuma amfani da fasahar zamani wajen kula da iyakoki.
Ribadu ya jaddada muhimmancin amfani da na’urorin tantance bayanai ta hanyar fasahar zamani, tsarin bayanan kula da iyakoki da kuma fasahar gano mutum ta hanyar bayanan halitta (biometric systems) domin inganta tsaro.
Ya kuma bukaci a kara zuba jari a yankunan kan iyaka ta hanyar samar da ayyukan raya kasa da damar tattalin arziki domin hana mazauna yankunan fadawa hannun masu aikata laifuka.
A nasa bangaren, Akpabio, wanda Sanata Ahmed Lawan ya wakilta, ya ce Najeriya na fuskantar kalubale masu yawa sakamakon tsawon iyakokinta na kasa da ruwa, wanda hakan ke saukaka safarar makamai, shige da ficen ba bisa ka’ida ba da kutsen miyagu.
Ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara saka jari wajen sa ido, inganta kayan aiki, karfafa hadin gwiwar hukumomi da amfani da fasahohin zamani domin kare iyakokin kasar.
Akpabio ya kara da cewa babu wani ci gaba mai dorewa da za a samu ba tare da zaman lafiya da tsaro ba, yana mai kira ga gwamnati, hukumomin tsaro, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya, kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai wajen kare Najeriya.
Tun da farko, shugaban riko na AANDEC, Commodore Amatare Kpou mai ritaya, ya bayyana cewa taken taron na bana mai taken “Karfafa Tsarin Tsaron Iyakokin Najeriya Domin Zaman Lafiyar Kasa” ya zo a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar matsalolin safara ba bisa ka’ida ba, fataucin bil’adama da sauran laifukan ketare iyaka.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa shawarwarin da za su fito daga taron za su taimaka wajen samar da ingantattun manufofi da dabarun tsaro domin gina Najeriya mafi aminci da kwanciyar hankali.