Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya bayyana damuwarsa kan karuwar hare-haren masu lalata kayayyakin gwamnati a Jihar Neja, inda ya ce wasu bata-gari sun lalata sassan hasumiyoyin wutar lantarki guda 14 na layin wutar 132KV da ke yankin Lambata a karamar hukumar Gurara.
Babban Manajan TCN na Yankin Abuja, Musa Shuaibu, ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar tare da sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da kungiyoyin sintiri a Lambata.
A cewarsa, layin wutar da aka lalata yana daga cikin tsofaffin muhimman hanyoyin isar da wutar lantarki daga Shiroro zuwa Minna, Bida, Suleja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda aka gina tun sama da shekaru 40 da suka gabata.
Shuaibu ya ce masu lalata kayayyakin suna sare igiyoyin wutar ne domin sayar da su a matsayin karafa, lamarin da ya jawo babbar asara ga gwamnati tare da kawo cikas ga samar da ingantacciyar wutar lantarki.
Ya bayyana cewa gyaran sassan da aka lalata zai ci TCN akalla Naira miliyan 32 idan kamfanin ne zai gudanar da aikin kai tsaye, yana mai cewa kudin da za a kashe wajen gyaran ya kamata a yi amfani da su wajen inganta harkar lantarki da samar da karin ayyukan ci gaba.
Jami’in ya gargadi al’umma kan hadarin da ke tattare da lalata layukan wutar lantarki, yana mai cewa ragowar lantarki a wasu lokuta na iya haddasa mutuwar mutane ko dabbobi da suka kusanci wuraren da aka lalata.
Ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da jami’an tsaro da su hada kai wajen gano masu hannu a wannan aika-aika domin kare muhimman kayayyakin gwamnati.
TCN ta bayyana cewa akalla mutane 19 da ake zargi da lalata kayayyakin lantarki a yankin Abuja suna tsare a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da ake shirin gurfanar da su a kotu.
Kamfanin ya ce lalata layukan wutar lantarki na ci gaba da zama babbar barazana ga samar da wuta a Najeriya, tare da haddasa asarar kudade masu yawa da kuma jinkirta ci gaban masana’antu da tattalin arziki.
