Gwamnatin Jihar Kebbi ta ayyana ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026, a matsayin ranar hutu ga daukacin ma’aikatan gwamnati da al’ummar jihar domin murnar fara sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH.
Sanarwar ta fito ne bayan amincewar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, wanda ya ba da umarnin rufe dukkan ofisoshin gwamnati a ranar domin bai wa al’umma damar gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Hijira cikin walwala da ibada.
Babbar Sakatariyar Ma’aikata ta jihar, Hajiya Hafsat Tune, ta bayyana cewa hutun zai fara aiki daga ranar Talata, yayin da ake sa ran ma’aikata za su koma bakin aikinsu a ranar Laraba, 17 ga Yuni, 2026.
Gwamnatin jihar ta ce hutun na daga cikin matakan girmama muhimmancin sabuwar shekarar Musulunci, wadda ke tuna wa Musulmi tarihin Hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makkah zuwa Madina, lamarin da ya kasance babban jigo a tarihin addinin Musulunci.
Gwamna Nasir Idris ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar 1448AH, tare da kira gare su da su ci gaba da yin addu’o’i domin zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da ci gaban jihar Kebbi da Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma bukaci jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani kan darussan Hijira kamar haƙuri, sadaukarwa, juriya da biyayya ga Allah, domin samar da al’umma mai cike da zaman lafiya da ci gaba.
Gwamnatin jihar ta yi fatan sabuwar shekarar Musulunci za ta zo da albarka, cigaba da kwanciyar hankali ga al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya.
