Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta biya sama da Naira biliyan 700 na basussukan da ake bin ta ga ‘yan kwangilolin cikin gida a watannin baya-bayan nan, a wani mataki na rage tarin basussuka da kuma farfaɗo da harkokin tattalin arziki.
Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Efe Ovuakporie, ya fitar a ranar Litinin, inda ta ce an amince da biyan kuɗaɗe ga fiye da ‘yan kwangila 1,240 daga ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban.
Sanarwar ta ce Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arzikin Ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya amince da biyan kuɗaɗen bayan an gudanar da bincike da tantance dukkan da’awar bashi domin tabbatar da sahihancinsu.
A cewar ma’aikatar, an bai wa waɗanda ake binsu Naira miliyan 100 ko ƙasa da haka fifiko a wannan zagayen biyan kuɗi.
Ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wa kamfanoni da dama su koma wuraren ayyukansu, su biya ma’aikata albashi, su daidaita bashin masu samar musu da kayayyaki tare da ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa a cikin watan Mayu kaɗai, an gudanar da mu’amalolin biyan kuɗi da suka kai kimanin Naira biliyan 436.6, lamarin da ya nuna ƙoƙarin gwamnati na hanzarta biyan basussukan da ake bin ta.
Ta jaddada cewa gwamnati na ci gaba da aiwatar da tsarin kula da kuɗaɗen jama’a cikin gaskiya da rikon amana tare da tabbatar da biyan dukkan haƙƙoƙin da aka tabbatar da sahihancinsu.
Haka kuma, ma’aikatar ta ce wannan biyan kuɗi zai ƙara ƙarfafa amincewar ‘yan kwangila, masu samar da kayayyaki da sauran masu hulɗa da gwamnati, tare da taimakawa wajen kare ayyukan yi da kammala muhimman ayyukan raya ƙasa
