Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu beli na Naira miliyan 100 daga Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta bayar da umarnin, inda ta ce dole ne El-Rufai ya gabatar da mutum guda a matsayin wanda zai tsaya masa, wanda shi ma zai kasance da irin wannan adadi.
Kotun ta kuma shar’anta cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance mazaunin Maitama ko Asokoro a Abuja, sannan ya ajiye asalin takardar mallakar gida (Certificate of Occupancy) a kotun.
Haka kuma, dole ne mutumin ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya mai matsayi bai kasa Grade Level 17 ba, tare da gabatar da shaidar albashi na akalla watanni uku.
Kotun ta kara da cewa dole ne bankin wanda zai tsaya masa ya tabbatar da ingancin takardun da aka gabatar ta hanyar wasika daga manajan bankinsa.
