Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2023, Dumebi Kachikwu, ya zargi tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da mamaye jam’iyyar tare da korar shugabannin da aka zaba bisa doka domin maye gurbinsu da mabiyansa.
Kachikwu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis, bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) amincewa da tarukan jam’iyyar da bangaren Mark ya shirya.
A cewarsa, kundin tsarin mulkin ADC ya tanadi cewa shugabannin jihohi ne ke da ikon gudanar da taruka da babban taron jam’iyya, amma bangaren Mark ya kafa kwamitocin wucin gadi domin karbe ikon shugabannin jihohi ba bisa ka’ida ba.
“Ina samun kira daga jihohi daban-daban cewa an ture su an kwace tsarin jam’iyyarsu,” in ji Kachikwu.
Ya kara da cewa wasu shugabannin jihohi da suka fara mara wa Mark baya daga baya sun gane cewa ana amfani da su ne kawai, bayan an nuna musu cewa ba su cikin mutanen da ake son su jagoranci jam’iyyar.
Kachikwu ya bayyana cewa kotu ta soke tarukan da bangaren Mark ya gudanar, inda alkalin ya bayyana taron a matsayin wanda ba ya bisa doka.
Ya ce wannan yunkuri wata hanya ce ta lalata ADC, yana mai cewa tun farko ya gargadi cewa jam’iyyar ba za ta taba amincewa da kwace ikonta ba.
A nasa bangaren, David Mark ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar cewa ADC za ta kasance a takardar zabe a shekarar 2027 duk da shari’o’in da ake yi, yana mai cewa bangarensa zai kalubalanci hukuncin kotu.
Ana sa ran Kotun Koli za ta yanke hukunci kan karar daukaka kara da Mark ya shigar dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar a yau da misalin karfe 2 na rana.
Kachikwu ya bukaci magoya bayan ADC su kasance cikin shiri, yana mai cewa har yanzu gwagwarmayar kare jam’iyyar ba ta kare ba.
