Gwamnatin Tarayya Tare da Faransa Za Su Inganta ICT a Jami’o’in Najeriya da Tallafin Naira Biliyan 38
A wani gagarumin mataki na bunƙasa ilimin zamani, Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta ƙaddamar da shirin ɗaukaka fasaha a jami’o’in ƙasa, da taimakon kudi daga Gwamnatin Faransa har €38 miliyan (Naira biliyan 38).
Wannan zai haɓaka tsarin e-learning, Wi-Fi, da kwamfuta a makarantu, tare da horas da malamai da ɗalibai a fannin fasaha.
Matasan Najeriya za su ci moriyar samun horo da ilimi a fannonin fasaha na zamani.
Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ganin Najeriya ta taka rawar gani a duniya ta fuskar ICT.
