Kungiyar masu kishin ‘kasa ‘yan jam’iyyar APC, ta zargi gwamnatin jam’iyyar NNPP da rashin iya gudanar da mulki a cikin shekaru biyu da suka gabata a jihar Kano, tana mai bayyana wa’adin a matsayin na koma baya da gazawa.
A wani taron manema labarai da kungiyar ta shirya a Kano, ta bayyana cewa gwamnati mai ci ta karbi kudaden masu yawa daga asusun kasafta arzikin ‘kasa da kuma wasu hanyoyin samun kudin shiga, amma hakan bai haifar da gamsassun ayyuka ko sauyi ba.
Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da rushe wasu gine-gine a fadin jihar Kano da suka hada da kantuna, gidaje da wutatetn Sana’a, tana mai cewa hakan ya faru ne ba tare da la’akari da tasirin zamantakewa da tattalin arziki ba.
Ta kara da cewa hakan ya saba da umarnin kotu kuma ya jefa dubban jama’a cikin halin ni-‘ya-su.
A bangaren ilimi, kungiyar ta ce duk da ware kaso 31 cikin 100 na kasafin kudin shekara, jihar ta gaza gyara makarantu, samar da malamai da kuma kayan aiki da ya kamata.
Ta kuma zargi gwamnatin da yin biris da umarnin kotu a wasu lamurra ciki har da rikicin masarautar Kano da batun ‘yancin kananan hukumomi.
