Ma’aikatar Sufuri ta Jihar Lagos ta gargadi masu ababen hawa da su yi hattara da saƙonnin bogi da kuma hanyoyin intanet na yaudara da ake aikawa direbobi da sunan hukumomin gwamnati.
Ma’aikatar ta bayyana cewa wasu masu damfara na aika saƙonnin SMS ko WhatsApp suna zargin direbobi da aikata laifukan hanya, sannan su tura musu hanyoyin intanet domin biyan tarar da ba ta gaskiya ba.
Ta shawarci direbobi da kada su danna hanyoyin intanet da ba su tabbatar da sahihancinsu ba, ko bayar da bayanan sirri da na banki, ko kuma yin biyan kuɗi ta wasu dandamali na ɓangare na uku.
Ma’aikatar ta ce direbobi za su iya tabbatar da sahihancin tikitin tara hanya ta hanyar Traffic Management Solutions (TMS) na gwamnatin jihar, inda za a iya bincika bayanan laifin hanya ta amfani da lambar mota da chassis, ko kuma Violation Number (VN) da ke kan tikitin.
Haka kuma, ana iya amfani da PAYVIS domin duba takardun biyan kuɗin da suka shafi abin hawa ta hanyar amfani da lambar mota ko lambar bill.
Gwamnatin jihar ta kuma gargadi jama’a kan shafukan bogi da ke jan hankalin direbobi da rangwamen tarar hanya. Ma’aikatar ta jaddada cewa Lagos ba ta bayar da rangwame kan tarar laifukan hanya, kuma kudaden tarar da gwamnati ta kayyade ba sa sauyawa.
Don haka, ana shawartar masu ababen hawa da su shiga shafukan hukuma da kansu maimakon danna hanyoyin da aka turo musu ta saƙonnin da ba su nema ba.
Shafukan da gwamnati ta amince da su sun hada da payvis.ng da tms.lagosstate.gov.ng.
Ma’aikatar ta kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani saƙo ko bukatar biyan kuɗi da suke zargi na damfara ga hukumomin da abin ya shafa.
Ga matsalar fasaha ta TMS, ana iya tuntubar ma’aikatar ta imel tmssupport@lagosstate.gov.ng ko kuma lambar waya 07000 TRAFFIC (07000 8723342).
