Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ba za ta kare duk wani mutum da bincike ya gano yana da hannu cikin mutuwar mutanen da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida, wadanda suka mutu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Niger.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya mika sakon ta’aziyyar gwamnatin tarayya ga Gwamnatin Jihar Niger, al’ummar Wushishi da iyalan wadanda suka rasu.
Mutanen da lamarin ya shafa an kama su ne a yayin wani samame da NSCDC ta gudanar domin dakile ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a yankin Wushishi/Lukoto na Jihar Niger a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026.
Idris ya ce yanayin da mutuwar ta faru na bukatar cikakken bincike mai zaman kansa, gaskiya da adalci, domin tabbatar da ainihin abin da ya faru kafin yanke hukunci kan wanda ke da alhaki.
Ya ce gwamnati ba za ta kare duk wanda bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu wajen mutuwar ba, amma bai kamata a riga an yanke wa kowa hukunci kafin kammala binciken ba.
Ministan ya bayyana cewa kare rayuwar ’yan Najeriya, mutuncinsu da hakkokinsu na asali na daga cikin muhimman nauyin da gwamnati ke da shi.
Wannan na zuwa ne bayan Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Niger, Suberu Aniviye, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A cewar Idris, matakin gaggawar da Ministan Harkokin Cikin Gidan ya dauka na nuna muhimmancin da gwamnatin tarayya ta bai wa lamarin.
Ya ce binciken zai gano hakikanin abin da ya faru, sannan gwamnati za ta dauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.
Gwamnan Jihar Niger, Umar Bago, ya tabbatar da cewa mutane 37 da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida sun mutu yayin da suke hannun NSCDC. Ya ce ana gudanar da binciken gawarwaki, gwaje-gwajen lafiya da autopsy domin gano musabbabin mutuwar.
Haka kuma, NSCDC ta kafa kwamitin bincike domin duba yanayin wadanda ake zargin a lokacin da aka kama su, tsawon lokacin da suka yi a tsare, yanayin wurin da aka tsare su da kuma irin kulawar lafiya da aka ba su.
Ya zuwa yanzu, ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar ba.
A wani bangare kuma, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya bukaci a tabbatar da adalci kan lamarin. Ya ce duk wanda bincike ya gano yana da alhaki ta hanyar aikata wani abu, cin zarafi ko sakaci, ya kamata a rike shi da cikakken alhaki.
Atiku ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa, cikakke kuma a bayyane, yana mai cewa iyalan wadanda suka mutu sun cancanci sanin gaskiya da samun adalci.
Ministan Yada Labarai ya bukaci al’ummar Wushishi da sauran mazauna Jihar Niger su kwantar da hankula tare da bai wa hukumomin da ke gudanar da bincike damar kammala aikinsu ba tare da katsalandan ba.
Ya kuma tabbatar wa iyalan wadanda suka mutu da al’ummar jihar cewa gwamnatin tarayya na tare da su a wannan lokaci na jimami, tare da addu’ar Allah Ya ji kan wadanda suka rasu, Ya kuma bai wa iyalansu da al’ummar Niger hakurin jure wannan rashi.
