Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Plateau da ke Bokkos, ta ayyana cikakken yajin aikin da ba shi da ƙayyadadden lokacin ƙarewa.
Ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta bayyana a matsayin gazawar mahukuntan jami’ar wajen warware buƙatunta guda shida cikin gamsasshen yanayi.
ASUU-PLASU ta sanar da fara yajin aikin ne ranar Laraba, bayan wani taron majalisar ƙungiyar, sakamakon ƙarewar wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa mahukuntan jami’ar tun ranar 11 ga Agusta.
A cikin wata sanarwa da shugabar ƙungiyar, Vincent D. Choji, da sakataren ƙungiyar, Lomka Kopdiya, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce har yanzu ba a warware buƙatunta ba duk da ƙarewar wa’adin.
Daga cikin buƙatun ƙungiyar akwai fara aiwatar da Contributory Pension Scheme, da kuma cikakken aiwatar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya da ASUU suka cimma a shekarar 2025.
Haka kuma, ƙungiyar ta nemi a biya malaman jami’ar bashoshin albashi daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Sauran buƙatun sun haɗa da samar da gidajen kwana masu tsaro ga ma’aikata, gina magudanan ruwa a kewayen katangar jami’ar domin magance matsalolin ambaliyar ruwa, da kuma dakatar da abin da ƙungiyar ta kira tsoratarwa ko muzgunawa shugabannin ƙungiyar.
ASUU-PLASU ta kuma nemi a biya malaman jami’ar bashin watanni 22 na 25/35 per cent wage award.
Ƙungiyar ta bayyana cewa majalisarta ta gamsu da cewa ba a magance ko ɗaya daga cikin buƙatunta guda shida yadda ya kamata ba.
Bayan samun amincewar Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta ASUU, ƙungiyar ta ce ta yanke shawarar fara yajin aikin.
Saboda haka, ta umarci dukkan mambobinta da su dakatar da dukkan ayyukan koyarwa da na ilimi har sai an ba da wata sabuwar sanarwa.
Yajin aikin dai na iya shafar harkokin karatu a Jami’ar Jihar Plateau da ke Bokkos, yayin da ake jiran matakin da mahukuntan jami’ar za su ɗauka domin ganin an warware matsalolin da ƙungiyar ta gabatar.
