Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Asrah 24 TV
  • Education
  • Health
  • Podcast
  • Politics
  • Sports
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
Facebook X (Twitter) YouTube WhatsApp Telegram
Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
ASRAH 24 MEDIA
Subscribe
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    FTSE Russell Ta Mayar Da Najeriya Matsayin Frontier Market, NGX Ta Ce Wannan Sabon Farko Ne

    August 27, 2026

    CBN Ta Ce Sauye-Sauyen Tattalin Arziki Sun Kafa Tubalin Ci Gaba Da Daidaiton Arzikin Najeriya

    August 6, 2026

    KOTU TA SAMU MACE DA LAIFIN YUNKURIN KASHE ƳAR SHEKARA 9 BAYAN TA YAUDARE TA ZUWA DAJI

    June 26, 2026

    KOTU TA KI SAKIN SOWORE, TA DAGE YANKE HUKUNCI ZUWA 30 GA YUNI

    June 24, 2026

    Cuba Ta Yi Watsi Da Kalam an Trump Na Cewa Ƙasar Za Ta Faɗi

    September 22, 2026

    Trump Ya Kulla Yarjejeniyar Tsaro Da Greenland Da Denmark, Amurka Za Ta Gina Sansanonin Soji Biyu

    September 22, 2026

    NIS Ta Yi Rijistar ’Yan Najeriya 8,552 a Ƙasashen Waje, Birtaniya Ta Fi Yawan Masu Amfana

    September 21, 2026

    Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah-wadai da Kai Hari Kan Ofishinta a Libya

    September 8, 2026

    Hatsarin Jirgin NAF A Ondo: ’Yan Sanda Sun Ce Babu Wanda Ya Tsira, Ana Ci Gaba Da Neman Ragowar Jirgin

    October 6, 2026

    NAF Ta Tabbatar Da Hatsarin Jirgin Soji A Ondo, Mutane 32 Suna Ciki

    October 5, 2026

    Anthony Kila Ya Musanta Zargin Cewa Shi ‘Farfesa Na Ƙarya’ Ne

    October 5, 2026

    Jirgin Sojin Sama Ya Yi Hatsari A Kusa Da Naval Base A Igbokoda, Fasinjoji 25 Da Ma’aikata 7 A Ciki

    October 5, 2026
  • Asrah 24 TV
  • Education

    NUT Ta Koka Kan Rashin Aiwatar Da Albashin Musamman Ga Malamai

    October 5, 2026

    WAEC Ta Naɗa Suleiman Kum A Matsayin Sabon Shugaban Ofishin Najeriya

    October 4, 2026

    Yadda Ilimin Kyauta Na Awolowo Ya Sauya Rayuwata — Tsohon Kakakin JAMB

    October 4, 2026

    Gwamnatin Tarayya Za Ta Zaɓi Malamai 14 Domin Kyautar Shugaban Ƙasa

    October 4, 2026

    Jigawa Ta Dauki Sabbin Malamai 2,020 Domin Cike Gibin Ma’aikata A Makarantu

    October 2, 2026
  • Health

    APM Terminals Ta Bukaci Gaggauta Rage Fitar Da Hayakin Carbon A Bangaren Jiragen Ruwa

    October 4, 2026

    Enugu: An Zargi Wani Matashi Da Kashe Budurwarsa Bayan Rigima Kan HIV

    October 3, 2026

    Ranar Zuciya Ta Duniya: Wayar Da Kai Da Gwaji Da Wuri Na Taimakawa Wajen Kare Zuciya

    September 30, 2026

    Najeriya Ta Yi Wa ’Yan Mata Miliyan 18 Rigakafin HPV Domin Kare Su Daga Sankarar Mahaifa

    September 29, 2026

    Edo Ta Mayar Da Gwajin Da Maganin Zazzabin Cizon Sauro Kyauta A Asibitocin Gwamnati

    September 23, 2026
  • Podcast
  • Politics

    Jamus Ta Kama Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri Kan Zargin Tura Sirrin Gwamnati Ga Kasashen Waje

    October 6, 2026

    BPE Ta Bukaci Ma’aikatan Gwamnati Su Wuce Aikin Tilas Don Inganta Ayyukan Jama’a

    October 6, 2026

    Shettima: Abokina Ya Samu Rijiyar Mai Ta Hanyar Gasa Ba Tare Da Alaƙar Siyasa Ba

    October 6, 2026

    BPE Ta Bukaci Ma’aikatan Gwamnati Su Wuce Aikin Tilas Don Inganta Ayyukan Jama’a

    October 6, 2026

    INEC Ta Ce Ba Za A Yi Zaɓen 2027 Da Ba A Kammala Ba

    October 6, 2026
  • Sports

    Alcaraz Ya Lashe Gasar Japan Open Bayan Dawowa Daga Rauni

    October 6, 2026

    Japan Open: Alcaraz Ya Kai Ƙarshe Bayan Ya Doke Munar A Wasan Zafi

    October 5, 2026

    Kocin Spain Ya Goyi Bayan Lamine Yamal Ya Zama Fitaccen Jarumin Kwallo

    October 4, 2026

    Yamal Ya Ci Gaba Da Cin Kwallaye, Spain Ta Doke Czech Republic 3-1

    October 3, 2026

    Barcelona Ta Nemi A Dage Wasan Mata Da Real Madrid Saboda Ambaliyar Ruwa

    October 3, 2026
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
ASRAH 24 MEDIA
Home » ADC Ta Bukaci Wike Ya Gargadi Shugaban Kuje Kan Kalaman Siyasa
Politics

ADC Ta Bukaci Wike Ya Gargadi Shugaban Kuje Kan Kalaman Siyasa

Asrah24 MediaBy Asrah24 MediaAugust 26, 20263 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
WhatsApp Image 2026 08 26 at 1.20.31 PM 1787747777

Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Okai Austin, ya yi kira ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya gargadi Shugaban Karamar Hukumar Kuje, Samuel Shekwolo, kan kalaman da ya bayyana a matsayin masu haddasa rarrabuwar kai da kuma ƙara zafafa rikicin siyasa a yankin.

Okai, wanda kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama ne, ya yi wannan kira ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Ya ce hakan ya biyo bayan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda ake zargin Shugaban Kuje da yin barazanar bibiyar tare da kai hari ga mutanen da ke sukar sa a kafafen sada zumunta.

An kuma zargi Shekwolo da gargadin mazauna yankin da ba sa goyon bayan jam’iyyar APC da su bar yankin.

Da yake mayar da martani kan kalaman, Okai ya bayyana su a matsayin “marasa dacewa kuma masu matukar hadari,” yana gargadin cewa irin waɗannan kalamai na iya haifar da tashin hankali idan hukumomin da abin ya shafa ba su ɗauki mataki cikin gaggawa ba.

Ya ce Abuja gida ce ga ’yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar, har ma da al’ummar ƙasa da ƙasa, don haka bai kamata a bar wani mutum ya ƙara dagula zaman lafiya da fahimtar juna ba.

Okai ya bukaci shugaban Kuje ya yi taka-tsantsan da kalamansa tare da mayar da hankali wajen inganta zaman lafiya, haƙuri da kuma haɗin kan mazauna yankin, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba.

Ya kuma jaddada cewa jami’an gwamnati, musamman shugabannin ƙananan hukumomi da ke da alhakin jagorantar al’umma a matakin ƙasa, ya kamata su kula da irin kalaman da suke yi domin kada su zama sanadin rarrabuwar kai.

A cewarsa, kasancewa shugaban ƙaramar hukuma bai kamata ya hana mutum nuna ladabi da kwarewar shugabanci ba.

Ya ce Kuje an san shi da zaman lafiya da haƙuri, don haka ya kamata shugabancinsa ya nuna irin waɗannan dabi’u.

Okai ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su duba kalaman da ake dangantawa da Shekwolo tare da tabbatar da cewa zababbun shugabanni da naɗaɗɗun jami’ai suna aiki wajen kare zaman lafiya da doka.

Ya ce bai kamata bambancin ra’ayin siyasa ya zama dalilin lalata zaman lafiya da zaman tare tsakanin mazauna Abuja ba.

Bugu da ƙari, ya bukaci Shekwolo ya yi koyi da shugabannin siyasa da suka shahara wajen warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da lumana, inda ya ambaci tsohon Sanatan Abuja, Philip Aduda, a matsayin misali.

Okai ya kuma roƙi Wike da sauran hukumomin da abin ya shafa da su shiga tsakani tun kafin lamarin ya ƙara tsananta, yana mai cewa shugabanci na gari yana buƙatar natsuwa, haƙuri da kuma mutunta ra’ayoyin da ska bambanta.

Share. Facebook Twitter Telegram WhatsApp
Previous ArticleASUU-PLASU Ta Tsunduma Yajin Aiki Mara Ƙayyadadden Lokaci Kan Buƙatunta
Next Article Ofishin Jakadancin Jamus Ya Gargadi ’Yan Najeriya Kan Masu Taimakawa Wajen Visa

Related Posts

Jamus Ta Kama Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri Kan Zargin Tura Sirrin Gwamnati Ga Kasashen Waje

October 6, 2026

BPE Ta Bukaci Ma’aikatan Gwamnati Su Wuce Aikin Tilas Don Inganta Ayyukan Jama’a

October 6, 2026

Shettima: Abokina Ya Samu Rijiyar Mai Ta Hanyar Gasa Ba Tare Da Alaƙar Siyasa Ba

October 6, 2026

BPE Ta Bukaci Ma’aikatan Gwamnati Su Wuce Aikin Tilas Don Inganta Ayyukan Jama’a

October 6, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Latest Posts

Jamus Ta Kama Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri Kan Zargin Tura Sirrin Gwamnati Ga Kasashen Waje

October 6, 2026

BPE Ta Bukaci Ma’aikatan Gwamnati Su Wuce Aikin Tilas Don Inganta Ayyukan Jama’a

October 6, 2026

Shettima: Abokina Ya Samu Rijiyar Mai Ta Hanyar Gasa Ba Tare Da Alaƙar Siyasa Ba

October 6, 2026

BPE Ta Bukaci Ma’aikatan Gwamnati Su Wuce Aikin Tilas Don Inganta Ayyukan Jama’a

October 6, 2026

Hatsarin Jirgin NAF A Ondo: ’Yan Sanda Sun Ce Babu Wanda Ya Tsira, Ana Ci Gaba Da Neman Ragowar Jirgin

October 6, 2026
Connect with us
  • Facebook
  • Twitter
  • YouTube
  • WhatsApp
  • Instagram
  • TikTok
Top Posts
Advertisement
© 2026 ASRAH 24 MEDIA. Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.